back to all blogs

All Blogs

Wasu masu kasuwanci da sana'oi sun bayyana mana yadda sukejin dadin amfani da manhajar Dillali

Jun 2022

4 mins read

Hausa

Wasu masu kasuwanci da sana'oi sun bayyana mana yadda sukejin dadin amfani da manhajar Dillali

Manhajar Dillali na taimakawa masu sana'oi 11,000 wajen sarrafa shige da ficen kuɗaɗen kasuwaninci bisa ingantacciyar tsari a kyauta. Wasu masu kasuwanci da sana'oi sun bayyana mana yadda sukejin dadin amfani da manhajar Dillal. Ga kaɗan daga cikin abunda suke faɗi:

HAUWA M BAKO - CEO HB GREENE ACRES FARMS

"Ina da gonan dankali, wanda ake nomawa sau daya a shekara. Muna buƙatan hanyar da zamu na bin diddigin dukkanin cinikayar da mukeyi musamman wanda kustomonin ke biyan rabin kudin kaya. Manhajar Dillali yana mana dukkan lissafe-lissafen . Abinda yafi burgemu shine yadda muke iya gane wani kustoma ne muke bin bashi da kuma wanda kasuwanci da shi muke samun riba"

GRACE IDEAWOR - ƳAR KASUWA

"Manhajar Dillali ya taimaka mini wajen bibiyar abokan kasuwancina. Yanzu haka na san duk wanda muka taɓa cinikayya da su, kuma cikin sauƙi zan iya duba duk waɗanda muka turawa resit na invoice amma har yanzu basu biyamu ba"

IMAM A - ƊAN KASUWA

"Ni ɗan kasuwa ne wanda baida lokacin kansa saboda a kullum mafi yanwan lokuta idan ba'a samen ina zaman turawa kostomoni resitai ba to kuwa za'a samen ina zaman duba bayanen kuɗaɗen da suka fita (expenses). Manhajar Dillali shine ya kawo min sauƙin wannan aiyukan. Ya taimaka min sosai na samu sauƙi da isheshen lokaci.

HADIYA - Mai Kamfanin Ruhminas Language Hub

Manhajar Dillali nada sauƙin sauƙewa , yanada kyau musamman ga masu ƙananan kamfani ko sana'a . Ina jin daɗin yadda zan iya tura resit na invoice ta kafar Whatsapp da kuma adireshin imel har kuma in tunatar da abokana nen cinikin na su biya bashi idan lokacin biyan yayi"

Fara yanzu kyauta